KITABUT TAUHID (Paketname: com.andromo.dev653890.app647048) wird von AdamsDUT entwickelt und die neueste Version von KITABUT TAUHID 2.4 wurde am 9. Juli 2020 aktualisiert. KITABUT TAUHID liegt in der Kategorie von Bücher & Nachschlagewerke. Sie können alle Apps von dem Entwickler der KITABUT TAUHID durchsuchen und 27 alternative Apps zu KITABUT TAUHID auf Android finden. Derzeit ist diese APP kostenlos. Diese App kann auf Android 4.1+ auf APKFab oder Google Play heruntergeladen werden. Alle APK/XAPK Dateien auf APKFab.com sind original und 100% sicher, schnell herunterzuladen.
Da sunan Allah mai yawan rahama mai yawan jinkai. Dukkan godiya ta tabbata a gareshi, kuma tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad (S.A.W) da iyalanshi da kuma sahabbanshi baki-daya. Bayan haka, wannan fassarar littafin “Kitabut Tauhid. ne, wanda Shehun malami Dr. Saleh bin Fauzan bin Abdallah Alfauzan ya wallafa, wannan malami fitaccan malami ne mamba ne a majalisar manyan malamai ta kasar Saudi Arebiya, kuma mamba a kwamitin dindindin na fatawa da kuma bincike akan ilimi. Wannan littafi na Tauhidi da wannan malami ya wallafa ya taba bangarori da dama wadanda ake matukar neman bayanan su a daidai wannan lokaci, zaka iya cewa littafin ya zo ne a daidai lokacin da ake matukar bukatarsa. Mawallafin littafin ya fara kawo mukiddima ne sannan ya biyo shi da babi-babi har guda hudu, sannan akar kashin kowanne babi akwai fasali-fasali da malam ya kawo. Babi na farko yana kunshe ne da fasali biyar, a yayinda babi na biyu kuma yake kunshe da fasali-fasali har goma sha-daya, shi kuwa babi na uku yana dauke ne da fasali-fasali har guda shida, ayayin da babi na karshe wato babi na hudu yake dauke da fasalai har guda hudu. Wannan littafi kamar yadda sunansa yake ‘Kitabut Tauhid’, kuma haka na Shehun malamin nan wato Sheikh Muhammad dan Abdulwahhab yake da ‘Kitabut Tauhid’ to amma sun yi tarayyane a suna amma sun sha banban a irin bayanan da suke dauke da shi, duk da bayanaine na tauhidi da kowanne yake da shi, saidai bangarorin da kowa ya dauka ya yi bayani daban-daban ne, saboda haka ana bukatar ka hada su duka ka mallake su, Allah ya anfanar da mu da su baki-daya. Lalle akwaimatukar bukatar a karantar da wannan littafi a makarantu da masallatai da kuma wuraran fadakarwa a kuma yada shi, saboda matukar muhimmancin da yake da shi da kuma yadda ya tabo wadansu bayanai da ake aikatawa a wannan lokacin da suke bukatar irin wadannan malamai su yi bayaninsu. Allah ya sakawa wannan malami da kuma wadanda suka yada wannan littafi Allah ya saka musu da alheri. Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad (S.A.W) da iyalanshi da kuma sahabbanshi baki daya. za kuma a iya samun wasu karatuttukan na wasu malam irin su sheikh jafar mahmud adam, sheikh albani zariya,sheikh ali isah fantami, shiekh kabir gombe. Akwai karatun alqur'ani na wasu manyan makaranta kamar complete quran offline by sheikh abdulrahman al-sudais mp3 beautiful quran recitation by sheikh maher almuquiy mp3 complete quran offline by shiekh abdolbasit mpe quran recitation by mishary alfasy mp3 offline and so on Don Allah idan har kaji dadin amfani da wannan littafi to ka taimaka kayi sharing din sa ga sauran yan uwa musulmai domin su ma su samu su amfana. kuma kada a manta ayi rating na wannan application .
APKFab.com und der Download-Link dieser App sind 100% sicher. Alle auf APKFab.com aufgelisteten Download-Links für Apps stammen aus Google Play Store oder werden von Benutzern eingereicht. Bei der App aus Google Play Store wird sie von APKFab.com in keiner Weise geändert. Bei der von Benutzern eingereichten App überprüft APKFab.com die Sicherheit der APK-Signatur, bevor sie auf unserer Webseite veröffentlicht wird.